‘Yan Dabar Siyasa Sun Farmaki Tawagar Atiku A Maiduguri
Daga Muhammad Maitela, Maiduguri
Kimanin mutum 74 ne aka kwantar a asibiti, motoci sama da 100 aka farfasa a wani farmakin da yan dabar siyasa suka kai wa tawagar dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a lokacin da ya ziyarci birnin Maiduguri ta jihar Borno a gangamin yakin neman zaben da jam’iyyar ta gudanar da yammacin ranar Laraba (yau).
Da yake mayar da martani kan wannan aika-aikar da yan dabar suka aiwatar, Kakakin kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP, Sanata Dino Melaye ne ya tabbatar da hakan a gangamin jam’iyyar a Maiduguri.
Sanata Dino ya kara da cewa, suna zargin jam’iyyar APC da kitsa kai wa ayarin dan takarar Shugaban kasar wannan farmaki ne a kokarin jam’iyya mai mulki a jihar Borno (APC) wajen ganin ko ta halin kaka ta hana gudanar da gangamin yakin neman zaben a jihar.
Ya koka da cewa, “Haka kuma mun lura da matakan su na jibge yan daba a wurare daban-daban don kai wa magoya bayanmu hari. Amma muna so mu tabbatar musu cewa babu wanda zai iya hana mu wannan taron.” Ya sha alwashi.
A wani martanin da ta mayar, jam’iyyar APC a jihar Borno ta musanta zargin da jam’iyyar PDP ta yi na amfani da yan dabar siyasa wajen kai wa Atiku Abubakar hari a ziyarar da ya kai a Maiduguri.
Shugaban jam’iyyar APC a jihar Borno, Ali Bukar Dalori, shi ne ya musanta ikirarin tare da bayyana cewa babu wani harin da yan barandan APC suka kai kan ayarin motocin jam’iyyar adawa a jihar.
Dalori ya shaida cewa Dino Melaye karya yake yi: “Na ji takaicin zargin da Dino Melaye ya yi cewa wasu magoya bayan APC sun kai hari kan ayarin motocin Atiku, a lokacin da suke Maiduguri domin yakin neman zaben shugaban kasa.
“Dukkanmu mun san cewa tun lokacin da Gwamna Babagana Zulum ya karbi ragamar shugabancin wannan jihar, ya haramta ayyukan bangar siyasa a fadin jihar Borno.
“Sannan kuma jam’iyyar APC mai bin doka ce, don haka ne a matsayinmu na gwamnati ba mu hana jam’iyyar PDP taron su ba. Kuma a iya sanin kowa ne babu PDP a Borno.”
“Kuma idan Dino Melaye ya rasa abin da zai gaya wa mutanen Borno ko kuma yadda za su yi zabe, ya kamata ya yi shuru kuma ya kama bakin shi ya daina kirkirar karya a kan jam’iyyarmu.”
