Najeriya Na Shigowa Da Sukarin Naira Biliyan 200 duk shekara.
Najeriya na shigowa da sukarin hadi da sauran sinadaran yin sukarin da darajar kudinsu ya ke kai naira miliyan dubu 200 duk shekara.
Shugaban kungiyar masu nomawa, sarrafawa da kuma sayar da reke ta Najeriya Colonel Abdulmummuni Aminu mai ritaya ne ya fadi hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina.
Ya ce shigowa da raken wanda Najeriya ke iya nomawa na ja mata asarar da gangan a wurin masayar kudaden kasashen waje.
Kamar yadda ya bayyana, Najeriya nada dukkan abubuwan da ake bukata wurin samar da sugan.
Abdulmummuni Aminu ya yi nuni da cewa, ana shuka rake a dukkan sassan Najeriya masamman ma a yankin arewacinta duba da kyawon yanayin wurin.
Ya bada misali da jihohin Katsina, Kano, Kaduna, Jigawa, Gombe, Nasarawa, Kwara da kuma jihar Adamawa da ke noma rake mai ɗunbin yawa.
Shugaban kungiyar ya ce kaso 2 na kayan da ake yi a duniya na bukatar zaki, wanda kuma ake samu daga rake.
Saboda haka ya yi kira ga manoman Najeriya su mike tsaye wurin magance kalubalen da ake fama da shi, tare da samar da kayan gonar da suka yi ƙaranci a cikin kasar don ganin ana fidda ma ƙasashen duniya.
