Mun Shirya Tsaf Zamu Yi Wa APC Korar Kare- Hon. Ɗanlami Kurfi
Daga Katsina City News
Tsohon ɗan Majalisar tarayya a ƙananan hukumomin Kurfi da Dutsinma Alhaji Ɗanlami Kurfi ya bayyana cewa nan da watanni kaɗan za suyi wa jam’iyyar APC zigidir, su yi mata korar kare.
Ya bayyana haka ne, a wata tattaunawar da yi ‘yan jaridu a ofis ɗinsa da ke Katsina.
Ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa ya bayyana cewa, PDP a matakin jiha da kuma ƙasa suna ta tattaunawa da jiga jigan APC da aka ci amanarsu da waɗanda aka ɓatawa rai.
Ɗanlami yace, da yawan su, sun ayyana lokacin da zasu shelanta ficewarsu. Don haka fitar zata riƙa kamawa lokaci zuwa lokaci ne, wasu ma sai a daren zaɓe.
Haka kuma Ɗanlami, ya ƙara da cewa daga cikin ‘yan APC wasu, za suyi zaman su a cikin ta suyi ma PDP aiki lokacin zaɓe.
Daga nan sai ya misalta jam’iyyar APC da jirgin da ya fashe a tsakiyar teku kuma ya fara nutsewa, yace abin da ya rage wajen tsira, itace jam’iyyar PDP.
Ɗanlami yayi ƙira ga al’ummar Katsina, su san azabar da suke sha na rashin tsaro, su kori jam’iyyar APC su kuma zaɓi PDP
