September 18, 2026

Gwamna Matawalle Ya Tabbatar Da Dokar Kisa Ga Masu Bada Rahotan Sirri Ga ‘Yan Bindiga

0

Daga Hussaini Ibrahim

Gwamnan jihar Zamfara Hon Bello Matawallen Maradun ya sanya hannu da tabbatar da dokar da ‘Yan majalisar Dokokin jihar tayi na Kisa ga wanda aka kama da hannu cikin ‘Yan Bindiga Masu Garkuwa da mutane da masu ba ‘yan Bindiga rahotan siri a Zamfara.

Matawallen Maradun ya sanya ma dokar hannu ne ayau bayan Shugaban Majalisar dokokin jihar Muazu Magarya ya gabatar masa da Dokar a gidan gwamnatin da ke Gusau.

A cikin dokar akwai ɗaurin rai da rai ga masu satar shanu. Kuma za’a kafa akwati na amsar koke daga jama’a a gaban gidan gwamnatin dan zamu nasara kawo karshen ‘Yan Bindiga da masu Garkuwa da mutane.

Gwamna Matawallen yayi kira ga jama’a da suji tsoran Allah wajan bada bayani siri a cikin wannan akwati.

Shugaban Majalisar dokokin jihar Zamfara, Hon Muazu Magarya ya bayyana cewa, sunyi waɗannan dokokin ne dan samarwa al’ummar jihar Zamfara mafita me ɗorewa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *