Yan Ta’adda Sun Harbe Daya Daga Cikin Fasinjan Jirgin Kasan Kaduna Da Aka Sace A Kaduna.
Bayan mako guda da jagoran sasantawar da aka naɗa don ganin an sako fasinjan jirgin Kaduna da aka yi garkuwa da su, Malam Tukur Mamu ya koka kan rashin lafiyar sauran fasinjojin da aka sace saboda sarin macizai, ya kuma bayyana cewa ɗaya daga cikin yan ta’addan ya harbe Mohammed Al’Amin dake zama cikin mutanen da aka yi garkuwa da su.
A cewar Mamu, wanda shi ne mawallafin jaridar Desert Herald da ke Kaduna, ya bayyana cewa sahihan bayanai da suke da shi sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin din da ta gabata yayin wata musayar wuta da aka yi a dajin tsakanin masu garkuwa da mutanen da ke gadin wadanda lamarin ya rutsa da su don hana su rugawa, inji majiyar Popular News Hausa ta Leadership.
Idan dai za a iya tunawa, kungiyar ta’addancin nan ta Ansaru da ta kai hari kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris tare da yin garkuwa da fasinjojin, ta yi barazanar hana su abinci da kuma kashe ɗaya bayan ɗaya.
Sai dai bayan tattaunawa da kungiyar tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya, Mamu ya samu damar kwantar musu da hankali domin su janye wannan tunanin.
Ya kara da cewa dole ne gwamnati ta shirya daukar cikakken alhakin rashin daukar mataki cikin gaggawa idan wani abu mara dadi ya faru.
