Me Ke Shirin Faruwa Da Maryam Hiyana?
Daga MUKHTAR YAKUBU.
Wani abu da ba a saba gani ba a game da tsohuwar Jaruma Maryam Usman Hiyana da Kuma ya faru a Yan kwanakin nan ya jawo surutu tare da saka ayar tambaya a game da lamarin.
Ba wani abu ba ne kuwa sai wani sabon salo na bayyanar wasu sabbin hotunan ta na Video a Shafin Tik Tok, shafin da a ke ganin sa a matsayin wata kasuwar Bajekolin karuwanci ne da nuna wa duniya irin rashin kunyar da mace ta kware da shi.
Mutane da dama suna tambayar ko dai auren Maryam Hiyana auren ta ya mutu ne ta bude wata Sabuwar rayuwa a Shafin Tik Tok?
To sai dai binciken da muka yi wata majiya ta kusa da Hiyana din ta shaida mana cewar wata kawar ta ce ‘yar Maiduguri ta rinka Dora hotunan, a Shafin ta Kuma da haka ne ya bazu a duniya. Amma dai yanzu an yi Mata magana ta cire hotunan.
Sai dai abin da mutane suke tambaya shi ne. Me ya hada su da kawar? Yaushe suka hadu su ke kawancen?
Me take so ta cimma a Kan yada hotunan Hiyana din?
Me ya hada kawancen na su da har ta samu damar baza hotunan ta a Tik Tok?
Lokaci da yanayi ne kawai zai bada amsar tambayoyin.
