Matashi Ɗan Shekara 23, Abdullahi Sidi Ya Bayyana Dalilan Da Yasa Ya Fito Takarar Shugaban Matasan APC na Kasa
Daga Salisu Hamisu Ali
Abdullahi Sidi Ali Mai shekaru 23 ya bayyana dalilan da yasa yake neman takarar shugabancin matasa na jam’iyyar APC na kasa.
Abdullahi Sid ya ce dokar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu a shekarar 2018 ta “Not Young To Run” ce ta ja hankalinsa wajen shiga zaben neman shugabancin matasan.
Matashin wanda dan asalin jihar Kano ne ya bayyana hakan ne a yau Litinin yayin tattaunawa da jaridar Prime Time News.
“Babban abinda yaja hankalina shi ne wannan doka da shugaban kasa ya sanyawa hannu a 2018 wacce ake cewa Not Young To Run. Wato babu kankanta a neman shugabanci a kasa. Wannan abun yana daga cikin abinda yasani neman wannan kujera ta shugaban matasa tun da daman kujerar ta matasa ce”.
Dangane da batun yadda matashi dan shekara 25 ya zama shugaban matasa na jam’iyyar hamayya ta PDP kuwa, dan takarar ya ce dole ce ta sanya jam’iyyar adawar bawa matashi dama, kuma suna da tabbacin hakan zai faru a jam’iyyar APC.
” Ita kanta jam’iyyar PDP lokaci ne ya kure mata, ta ga cewa idan bata janyo matasa ta sanya su cikin wannan lamari, to abu ne wanda tana bukatar mulki dole sai ta yi haka”
Dangane da shirin shiga zaben da jam’iyyar ta tsara gudanawar a watan Fabarairu kuwa, matashin ya ce sun shirya shiga zaben kuma suna da tabbacin samun nasara.
Daga karshe ya bayyana aniyarsa ta kawo sauyi a fannin siyarsar matasa da zarar ya samu nasara.
