Matasan APC A Zamfara Sun Fito Da Sabon Salon Yakin Neman Zaɓen 2023
Daga Hussaini Ibrahim.
Matasan jami’yyar APC na jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin shugaban matasan jiihar Hon. Musa Idiris Ardo sun fito da sabon salon yakin cin zaɓe ,na jawo matasan jam’iyyun adawa kuma sun shirya tsaf domin samun nasara cin zaɓe tun daga na shugaban ƙasa Ahmad Bola Tinubu da na gwamna Bello Muhammed Matawallen Maradun da na Sanatoci da ‘yan Majalisar Wakilai da na Majalisar Dokokin jihar ta Zamfara.
Shugaban matasan Musa Ardo ne ya tabbatar da haka a lokacin taron shugabanni matasan da masu ruwa da tsaki na jami’yyar APC a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Hon Ardo ya tabbatar wa shugaban matasan na yankin Arewa Kwamaret Abduhamid Umar ( Oscer) cewa a Zamfara matasa ne ke bada kuri’a tamani bisa ɗari kuma da yardar Allah yadda wata jam’iyyar adawa bata taɓa cin zaɓe ba, a Zamfara, jami’yyar APC ce ke cin zaɓe’ wannan karon ma zamu yi masu shal da yardar Allah .Inji Musa Ardo.
Ardo ya kuma tabbatar da cewa, sunyi shiri na musamman domin ganin sun ƙara samun karɓuwa ga sauran matasan jam’iyyun adawa da ke faɗin jihar Zamfara.
A asa jawabin babban bako , shugaban Matasan Na Yankin Arewa, Kwamaret Abduhamid Umar (Oscer) ya jinjinwa shugabannin Matasan na jihar Zamfara, akan sabon salon yakin Neman nasar zaben Mai zuwa,wajan kokarinsu na jawo Matasan Jamiyyun adawa zuwa Jamiyyar APC dan kara samun narara cin zabubuka a Shekara ta 2023.
Kwamaret Abduhamid Umar Oscer,ya kuma tabbatar da cewa, “Idan Matasan suka zabi Alhaji Ahmad Buoa Tinubu a matsayin shugaban ƙasa lallai zasu dara dan shi kullun burinsa shine yadda matasa zasu samu aikin yi da cigaban su dan sun amfanar da ƙasar mu wajan cigaban ta”.inji Kwamaret Oscar.
Kuma ya tabbatar masu da cewa, Idan jam’iyyar APC da samu gagarumar nasara a zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni da ‘yan Majalisar Dattawa da na Wakilai da na jihohi lallai ƙasa zata canza wajan cigaban rayuwar al’umma.
