Gwamnatin Jihar Zamfara Da Jami’an Tsaro Sun Hana mu Dakat -Jam’iyyar PDP A Jihar Zamfara
Daga Hussaini Ibrahim
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Zamfara Hon. Muktar Lugga ya koka akan zargin gallazawar da jami’an tsaro da gwamnatin jihar Zamfara ke ma “ya ‘yan jami’yyar kuma tana farautar su zuwa gidajan Yari ba tare da laifin komai ba.
Hon Lugga ya bayyana haka ne a taron manema labarai da aka gudanar a shalkwatar jam’iyyar ta jihar da ke Gusau .
Shugaban ya zargi gwamnatin jihar Zamfara tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro da kame mambobinsu bisa zargin karya dan cutar da su ba tare da laifin komi ba.
Ya Kuma bayyana cewa ɗan takarar Sanatan Zamfara ta tsakiya na jam’iyyar PDP kuma tsohon Ministar yaɗa labarai, Alhaji Ikra Aliyu Bilbis yau sati biyu ya na tsare a gidan Yari tare da gurfanar da shi gaban kotu kan zargin ɗaukar nauyin ‘yan bangar siyasa wajen lalata Allunan tallan jam’iyyar APC a babban birnin jihar.
Ya ƙara da cewa hatta sharuɗan da kotu ta sanya na belinsa ya saɓawa tsarin mulki Najeriya, abin na neman zaman rashin adalci inda aka ce sai ya kawo manyan sakatarori waɗanda ke bakin aiki a yanzu ne zai amshi belin Ministan.
Ya ce yin hakan ya saɓawa hankali da doka da kuma ƙa’idar shari’a, wanda bashi da gwamnati ya ya zai kawo ma’aikacin gwamnati ya yi belin ɗin ɗan adawa.
Hon. Lugga ya kuma koka da yadda aka kama tare da daure tsohon jakadan ƙasar Guinea Kanal Mai Riga Muhammad a matsayin wanda bai yi laifin koma ba sai ɗan ya jami’yyar PDP.
“Tsohon jakadan ya kwashe sama da wata guda a gidan Yari kuma shari’ar sa tana tafiyar hawainiya inda haryanzu anayi mana barazana daga gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin gwamna Bello Muhammad Matawalle tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro na kama duk wanda ya fito fili ya ayyana shi ɗan jami’yyar PDP ne a Zamfara.
Shugaban ya yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, da jami’an tsaro na jihar da kuma babban sufeton ‘yan sanda da su yi wani abu akan halin da jam’iyyar PDP da mutanan ta ke ciki na matsi da takurawa daga jami’an tsaro da gwamnatin jihar Zamfara ke masu.
Sannan ya ƙara da cewa duk da doka ta ba su damar aiwatar da harkokin su na jami’yyar a faɗin jihar amma gwamnatin jihar haɗin gwiwa da jami’an tsaro suna hana su aiwatar da harkokin su kamar sauran ‘yan ƙasa.
Ya kuma yi kira ga ƙasashen Duniya da gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da su sa baki a cikin lamarin domin samun zaman lafiya don a halin yanzu dimokuraɗiyya na fuskantar barazana a jihar Zamfara.
“PDP jam’iyya ce mai bin doka da oda a jihar Zamfara kuma muna kira ga magoya bayanmu da su kwantar da hankalin su mu ‘yan ƙasa ne kuma masu bin doka da oda ne a kodayaushe’
