November 18, 2026

Matasa Sun Banka Ma Barawon NAPEP Wuta, Yayinda Yan Sanda Suka Ceci 2 A Akwa Ibom.

0

Wasu fusatattun matasa sun banka ma wani da ake zargin barawon NAPEP ne wuta a yankin Itam da ke karamar hukumar Itu a jihar Akwa Ibom.

A cewar wani Nsifon Anwangaobong, wani mai sayar da kayan abinci a shahararriyar kasuwar Itam International da ke kusa da Uyo, babban birnin jihar, ‘barayin sun yi kokarin tserewa da NAPEP ɗin, amma aka yi rashin sa’a wasu matasa ‘yan bijilanti na Itam suka kama su. wanda ya tabbatar da kashe shi kafin isowar jami’an ‘yan sanda daga Itam dake kusa da su.”

Sai dai hedikwatar ‘yan sandan jihar da ke Ikot Akpanabia, ta tabbatar da ceto mutane biyu daga konewa, bayan da aka kama su da wasu kayayyaki da suka hada da janareta da aka sace a Coci, da kwalaben Campari Brandy guda biyu da aka sace a wani babban kanti, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Leadership ta bayyana.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *