September 18, 2026

‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Hukuncin Korar Jami’ansu Da Suka Tafi Da Wanda Ake Zargi Ya Ciro N1,190,000.00 A Banki A Kwara.

0

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da hukuncin korar jami’anta a jihar Kwara.

Kakakin rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi a lokacin da ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, ya ce kwamitin yin bita ya bada shawarar gurfanar da jami’an bisa aikata laifin hada baki, sata da kuma watsa muggan labarai akan rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Jami’an biyu da aka kora, Sajan Shola Akano da Kofur Babatunde Glorious sun yi zargin cewa, an kore su ne bisa rashin adalci bayan sun ƙi karbar cin hancin da zai shafi sakamakon bincike.

Wani bangare na sanarwar ya kara da cewa, “Rundunar ‘yan sandan Najeriya na son yin magana akan wani faifan bidiyo mai dauke da wasu jami’an ‘yan sanda da aka kora, Sajan Shola Akano da Kofur Babatunde Glorious, daga rundunar ‘yan sandan jihar Kwara da kuma buga wani labari akan wata jarida mai fitowa kullum ta kasa. A cikin wannan faifan bidiyo da labarin da aka wallafawa, jami’an na zargin cewa korar da aka yi musu daga aiki a hukumar ‘yan sandan Najeriya ba daidai ba ne, sakamakon kin karbar cin hancin da suka yi don sasanta lamarin da suke bincike. “Saboda haka, rundunar yan sandan Najeriya na son bayyana halin da ake ciki a kan korar da aka yi musu tare da tabbatar da sahihancin tsarin ladabtarwa bayan an sake bincikarsu.

“Kamar yadda binciken da sashen bincike na musamman na rundunar ‘yan sandan da ke Abuja ya yi, ya nuna dalla-dalla su biyun na Sgt. Akano da Kofur Glorious sun kasance a ofishin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, inda suke aikin amsar korafe-korafen jama’a da aka gabatar masu tsakanin jama’a da jami’an yan sanda kan rashin da’a da nuna rashin kwarewa. Abin takaici, yayin da ake gudanar da bincike an kawo kyas ɗin haɗa kai a aikata laifi da cin kuɗin shigar ciniki a watan Fabrairun 2020.

Sun yi rashin da’a wanda ya sa aka kore su aiki daga rundunar ‘yan sandan Najeriya. A lokacin da ake gudanar da bincike kan lamarin, mutanen biyu da ake zargi sun kama wasu mutane biyu – da mai suna Fatai Ridwan Olarewaju da kuma Awogbemi Samuel Olayinka, dalibin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Offa a Jihar Kwara.

“A ranar 7 ga watan Fabrairun 2020, jami’ansu sun tsara, tare da ɗaukar ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin mai suna Olarewaju, daga dakin aje mutane na ‘yan sanda inda aka tafi da shi zuwa bankin Zenith da ke titin Unity, Ilorin, suka sanya wanda ake zargin ya cire kudi har N1,190,000.00 daga asusunsa, wanda Kofur Glorious ya amsa. Bayan haka ne aka mayar da wanda ake zargin zuwa dakin aje mutune, daga bisani kuma aka bayar da belinsa a wannan rana, yayin da ba a bashi kudaden da aka ciro ba, wayoyin hannu guda biyu da sauran abubuwanshi.

Maimakon bin hanyar da ta dace, Sgt. Akano da Kofur Glorious sun ci gaba da neman karin kudi daga hannun wanda ake zargin don rufe kyas ɗin, inda suka ci gaba da hanyoyin tatsar kuɗi. Irin haka sun sabama ayyuka da ka’idojin jami’an ‘yan sanda kai tsaye, lamarin da ya sa Mista Fatai ya kai rahoton hakan ga mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da rundunar IGP X-Squad domin bincike. Daga baya kuma, an gabatar da tabbataccen hujjoji da suka haɗa da tattaunawa da aka yi ta wayar salula samfarin iPhone 11 Pro, don amfanin Corporal Glorious a lokacin shari’ar.

“Bisa cikakken nazari na shaidu da kuma shaidar dukkan bangarorin da abin ya shafa, an same su biyun da laifi kuma an kore su daga aiki a rundunar ‘yan sandan Najeriya. Ya kamata a lura da cewa, irin korafin da jami’an suka gabatar gaban kwamitin bincike #EndSARS da ke Ilorin, an tabbatar da korarsu ne bayan gudanar da cikakkiyar bita akan hujja da shaidu daga dukkan bangarorin bangarorin da abun ya shafa..”

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *