September 17, 2026

Masarautar Maska Ta Ziyarci ‘Yan Gidan Masarautar Da Suka Yi Shekaru Sama Da 100 Suna Gudun Hijira A Lere

IMG-20250225-WA0006

Masarautar Maska Ta Ziyarci ‘Yan Gidan Masarautar Da Suka Yi Shekaru Sama Da 100 Suna Gudun Hijira A Lere

Daga Hussaini Yero, Funtua

A ranar Lahadi ne 23/2/2025 masarautar Maskan Katsina ta ziyarci ‘Yan Gidan Masarautar da sukayi Hijira sama da shekaru ɗari daga garin Maskan zuwa Jihar Kaduna inda sukayi masauki a wani tsibiri da al’ummar garin ke kiransa Maskawa cikin Karamar Hukumar Lele.

Ziyarar ta kasance ne ƙarƙashin jagorancin Magajin garin Funtua injiniya Shehu Nuhu da Injiniya Isyaku Aliyu Maska.

A jawabin sa Alhaji Ibrahim Umar Masakawa wanda yanzu haka shine uba a Masakawa kakansu ɗaya da Muhammad Jaji, ya bayyana cewa sun samu baki daga fadar mai martaba Sarkin Maskan Katsina Hakimin Funtua domin sada zumuncin fiye da shekara ɗari.

sYa ce un kawo ziyarar ne domin gano zuri’ar ɗan uwan su wanda ake kira da Muhammad Jaji wato Atiku wadda ya baro Garin Maska ta jihar Katsina saboda rigimar sarauta wanda daga kƙrshe ya kafa Garin sama da shekaru ɗari.

Alhaji Ibrahim Umar Masakawa ya bayyana tarihin iyaye maza da mata da gwagwarmaya da suka sha wajan kafa garin Masakawan.

A karshe ya bayyana godiyar sa da wannan ziyara wanda ya ce ta karfafa zumunci ce kuma yau sun zo, sun gaida  gida tamkar suna cikin garin Maska ne.

Shima a nasa jawabin Jagoran tafiyar Magajin garin Funtuwa injiniya Shehu Nuhu ya tabbatar da cewa lallai kam sun zo gida da suke da tushen tsakanin kaka da kakanni kuma sunji daɗin tarbar da akayi masu da kuma yadda muka karu da tarihin kakanninsu.

Kuma wannan ziyara ta kara ma su kwarin gwiwa na nema danginsu a duk inda suke a faɗin ƙasar nan da wajan ta inji Magajin garin Funtuwa.

Mudassir Ibrahim ya bayyana jin dadinsa ganin ashes suna da tushen mai rasa wanda kuma ya wanzu a faɗin ƙasar nan ya kuma tabbatar da cewa za suyi iya ƙoƙarin su a matsayinsu na matasa ɗan zakulo dangin su a faɗin ƙasar nandan kyautata alaƙar zumunta a tsakanin mu .

About The Author