Mutane 600 Sun Amfana Da Tallafi Daga Gidauniyar Kabir Gafiya a Katsina
Gidauniyar Kabir Gafiya ta tallafawa mata da ƙananan Yara da marayu da masu buƙata ta musamman a ƙaramar hukumar Kaita ta jihar Katsina.
Da ake bikin kaddamar da bada tallafin shugaban gidauniyar kuma shugaban hukumar ilimin bai ɗaya na jihar Katsina Alhaji Kabir Magaji Gafiya ya bayyana cewa bada tallafin ya zama wajibi duba da buƙatun al’umma
Ya ƙara da cewa tallafin ya haɗa da kuɗaɗai da kuma kayan ‘yan makaranta da aka zaɓo daga gundumomi 10 da ke karamar hukumar Kaita domin tallafa masu .
Alhaji Kabir Gafiya ya ƙara da cewa tallafi zai haɗa da mata jawarawa da masu buƙata ta musamman da ɗalibai da kuma matasan jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Kaita baƙi ɗaya.
Alhaji Kabir Gafiya ya bayyana cewa an kirkiri wannan gidauniya ne domin a tallafawa ma buƙata a matsayin gudunmawarsa da zai baiwa al’umma a ƙarƙashin wannan gidauniya.
Haka kuma ya cigaba da bayanin cewa an ware kimanin naira miliyan 15 domin rarrabawa ga waɗannan mutane da aka ambata domin su amfana daga gidauniya da aka assasa domin al’umma.
“Da yardar Allah wannan tallafi zai taimaka wajen rage raɗadin talauci da al’umma ke fuskanta a ƙaramar hukumar Kaita da jihar Katsina baƙi ɗaya.
Dakta Kabir Gafiya ya yabawa gidauniyar gwagware da aka kafa domin tallafawa marasa karfi tare da nuna godiya bisa tallafin naira miliyan ɗaya da bada domin a ƙara bunƙasa wannan aikin alheri.
Tunda farko, da yake jawabi babban bako kuma gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa wanda mataimakin sa Malam Faruƙ Lawal Jobe ya wakilta ya nuna godiyar sa da irin wannan tallafin wanda ya ce yana daga cikin abubuwan da gwamnatin su ta sanya gaba.
Haka kuma ya yi ƙarin haske akan irin nasarorin da gwamnatin su ta samu musamman alƙawarin zaɓe da suka ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓen wanda ya ce zuwa yanzu sun taɓa kowane ɓangare.
Malam Faruƙ Lawal ya bayyana cewa cewa yanzu sun tallafawa mutane fiye da 25,000 a fadin jihar Katsina da suka haɗa da Mata da marayu da matasa da sauran al’umma.
A cewar sa, irin wannan tallafi da gwamnatin su ke yi wa al’umma tasa jam’iyyun adawa a jihar Katsina ba su da abin cewa a kakar zaɓe ta 2027
Malam Faruƙ Jobe wanda ya ce gwamnatin Malam Dikko ta yi abin a zo a gani da suka haɗa da hanyoyi da makarantu da asibitoci da ɓangaren ruwa sha da magudanan ruwa da sauransu a kasa da shekaru biyu da hawan su
Ya ƙara da cewa gwamnatin su ta ɗauki ma’aikata a ƙananan hukumomi guda 34,152 a ya yin da suka baiwa malaman makaranta aiki su kimanin 7,325 baya bada tallafi da aka yi a lokuta daban -daban ga mata da matasa wanda ya ce hakan ya maida jam’iyyun siyasa a jihar Katsina tamkar wani hunko a siyasa.
