September 18, 2026

Kungiyar ‘Yan Jihar Akwa Ibom Ta Nisanta Kanta Da Wani Labari Mai Cewa Ta Kwashe Mutanenta Daga Katsina.

0

Kungiyar ‘yan asalin jihar Akwa Ibom da ke zaune a jihar Katsina ta karyata wani labari dake cewa, yan asalin jihar ta Akwa Ibom sun fada cikin matsalar tsaro.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a Katsina, shugaban kungiyar Ubong Patrick ya bayyana labarin a matsayin wani yunkuri na tatsar jihar su kudi ta hanyar karama miya gishiri akan halin da tsaro yake ciki a jihar Katsina.


A nashi jawabin, sakataren kungiyar Dr. Aniefor Farncis ya bayyana damuwa kan gazawar gwamnatin jihar Akwa Ibom na bincika zargin da akayi kafin fara kwaso mutanen.

Ya bukaci jihar Akwa Ibom da jihar Katsina su tattauna batun tsakaninsu.

Shima a lokacin da yake yi ma manema labarai bayani a Katsina, mai ba gwamna shawara akan harkokin tsaro Ibrahim Katsina, ya yi nuni da cewa ba wani abu makamancin wannan a Katsina.

Haka zalika, makaddashin mai magana da yawun gwamnan jihar Katsina Malam Isa Ahmed ya bayyana cewa dukkan yan asalin jihar mazauna Katsina basu cikin matsala kuma suna gudanar da harkokinsu na yau da kullun.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *