An Kara Tsakanin Sojoji Da Jami’an Amotekun A Jihar Ondo Kan Kama Shanu.
An yi arangama tsakanin jami’an tsaron jihar Ondo na Amotekun da sojoji a Akure, babban birnin jihar a yammacin jiya Talata, kan kama shanu sama da 100 da suka karya dokar hana kiwo ta jihar.
Jami’an tsaron jijar sun kai samame tare da kama shanun bayan aka yi masu kiran gaggawa a yakin Oke Aro dake cikin birnin jihar bisa zargin cewa sun lalata gonkai.
Kamar yadda wani shaidar gani da ido ya bayyana, jami’an Amotekun sun hana wasu jami’an da ke 32 Artillery Bragade a Akure tafiya da shanun.
Sojin dai sun yi ikirarin cewa shanun oganninsu ne dake cikin bariki.
Jaridar LEADERSHIP ta bada rohotan cewa, a daidai lokacin da jami’an Amotekun ke kokarin kama shanun a yankin Alagbaka dake cikin jihar, wasu sojoji suka zo su kimanin goma cikin mota akori kura tare da hana a kama shanun.
Sojojim suka jajirce cewa, ba inda za a da shanun, saboda na oganninsu ne.
Amma kuma jami’an Amotekum suka tsaya kai da fata cewa, wannan shanu sun saba doka, don haka ya zama wajibi a kai su ofin don mai su ya zo ya yi belinsu.
Kuma rikici dai ya fara ne, bayanda aka fara masayar kalmomi masu, inda daga bisani aka ba hamutta iska akan titi.
Kamar yadda wani shaidar gani da ido ya bayyana, kafin a ankara, sun kama harbe harbe kan mai uwa da wabi, wanda hakan ne ya sa mutane suka kama gudun tsira da ransu.
An bayyana cewa, daga jami’an sojin sun ci karfin jami’an Amotekum, indaa harma suka kama biyu daga ciki jami’an na Amotekum.
Amma da aka tuntunbi kwamandan Amotekum na jihar Adetunji Adleye, sai ya ce wata yar matsala ce aka samu tsakanin jami’an biyu.
Adeleye ya ce, “An warware shi cikin ruwan sanyi”, ya kara da cewa “makiyayan da aka kama ne suka boye a karkashin sojoji don haifar da rashin fahimta tsakanin jami’an tsaro.”
Kwamandan ya kara da cewa an mika ma rundunar Amotekun shanun.
An kuma bayyana cewa an sako jami’an Amotekun biyu da aka kama.
