November 18, 2026

2023: PDP Zata Samar Da Shugaban Ƙasa Ta Hanyar Sasanci — Makinde.

0

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya ce dan takarar shugabaancin Najeriya karkashin tutur jam’iyar PDP zai kasance wanda kowa ke so.

Gwamnan wanda ya fadi hakan a lokacin da ya amshi bakuncin wata wata tawagar jam’iyyar da suka kawo mashi ziyara a gidan gwamnati, ya ce jam’iyar za ta tabbatar da ganin an fitar da dan takara ta hanyar sasanci.

Jaridar leadership ta ce, Makinde wanda ya amshi bakuncin tawagar jam’iyar masu neman shugabancin Najeriya, da suka hada da Dr. Abubakar Bakola Saraki, da gwmnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, da gwamna jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad, da tsohon ma’aikacin banki ka masanin tattalin arzuki

Muhammad Hayatudeen, ya ce masu ruwa da tsakin jam’iyar PDP za su tabbatar da ganin an yi sasanci wurin yin zaben fidda gwanin jam’iyar.

A wata sanarwa da sakataren yan jaridar gwamnan jihar ta Oyo Mr. Taiwo Adisa ya fitar, ta bayyaba cewa gwamnan ya sha alwashin yin aiki kafada da kafada da yan takarar don ganin an yi sasanci a wurin zaben fidda gwani.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *