Kungiyar SWAN Ta Taya Dr. Bishir Gambo Saulawa Murnar Samun Kwamishinan Wasanni A Jihar Katsina.
Kungiyar marubuta wasanni ta Najeriya reshen jihar Katsina ta taya sabon kwamishinan wasannin da cigaban jama’a Dr. Bishir Gambo Saulawa murna bisa nadin da akayi mashi.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar kwamarad Nasir Sani Gide ya sanya ma hannu.
Kamar yadda sanarwar tace, nada Dr. Bashir Gambo Saulawa a matsayin kwamishinan wasannin da cigaban jama’a abu ne da ya dace ta la’akari da gudumuwar da yake bayarwa wajen cigaban matasan jihar Katsina.
Sanarwar ta kuma yabama hangen nesan gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari bisa nada Saulawa domin ya jagoranci ma’aikatar ta wasanni.
Shugaban kungiyar ya bukaci kwamishinan da ya farfaɗo da harkokin wasannin gargajiya da sauran wasanni a fadin jihar a jihar Katsina.
