Kungiyar Sa Kai Ta Bakiyawa Ta Bukaci Gwamnatin Jihar Katsina Mai Zuwa Ta Yi Tafiya Da Mutanen Yankin.
Sakataren kungiyar ma’aikatan sa kai na Bakiyawa ya yi kira ga gwamnatin APC mai zuwa a jihar Katsina ta saka mutanen yankin a cikin naɗe-naɗen siyasa.
Haka zalika, Malam Imran Sa’adu Bakiyawa ya yi ga gwamnatin mai zuwa ta duba yiyuwar shimfida hanyar Bakiyawa-Tsauri-Kurfi don bunƙasa tattalin arzikin mutanen yankin.
Ya ce mutanen yankin sun yi ma jam’iyar APC ruwan kuru’u duk da matsalar tsaron da suke fuskanta.
Kamar yadda ya bayyana, @ ya albarkaci al’ummomin Bakiyawa da mutanen dake taimakawa domin ci gaban jihar nan.
Ya taya zaɓaɓɓen gwamnan jihar Katsinan Dikko Umaru Radda da sauran waɗanda suka yi takara murnar samun nasarar lashe zabe.
