Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Civil Defense 3 A Jihar Imo.
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, a ranar Litinin ɗin nan sun kashe jami’an hukumar tsaro ta farin kaya ta Civil Defense guda uku a jihar Imo.
Lamarin da ya faru a kasuwar EkeIsu da ke unguwar Obiangwu a karamar hukumar Ngor Okpala a jihar, ya jefa al’ummar cikin rudani.
Wata majiya ta al’ummar da ba ta so a ambaci sunan ta, ta shaida wa Wakilin jaridar Leadership dake zama majiyar Popular News Hausa cewa, an kai harin ne da sanyin safiyar Litinin din nan.
Ya ce jami’an Civil Defense din na cikin mota ne a lokacin da maharan suka yi musu kwanton bauna suka kashe su.
A cewarsa, jami’an tsaro sun mamaye al’ummar inda suka ce suna kamen matasan al’ummar.
Ya jaddada cewa an kwashe gawarwakin wadanda aka kashen tare da kai su dakin ajiye gawa da ke kusa.
Majiyar ta kara da cewa, “An kashe jami’an hukumar uku da safiyar yau a kasuwar EkeIsu da ke unguwar Obiangwu a karamar hukumar Ngor Okpala ta jihar Imo. An yi musu kwanton bauna yayin da suke cikin motarsu kuma aka kwashe gawarwakinsu. Kamar yadda muke magana, jami’an tsaro sun mamaye al’umma suna kama matasa.”
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma jaddada cewa jami’an tsaro sun je wurin domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
