kungiyar Katsina United Ta Gayyaci Yan Wasa Masu Taka Leda A Cikin Gida Domin Tantance Su.
Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafar Katsina United ta gayyaci yan wasan da ke cikin jihar 120 domin tantance su zuwa wanda za ta bada damar gwada hazakarsu.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in watsa labarai Nasir Gide ya fitar.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, za a gudanar da aikin tantancewar ne tsakanin ranar Laraba 28 ga watan Satumba zuwa ranar 6 ga watan Oktoban wannan shekarar ta 2022.
Sanarwar ta ambato Daraktan kungiyar kwallon kafar ya na cewa, an bada gurabe ga yan wasan ne duba da abinda suka ƙware akanshi na tawagar kwallon kafar da suke bugama wasa a kananan hukumominsu.
Saleh Yusuf ya yi nuni da cewa, karamar hukumar Katsina ce ke da gurabu 20 na yan wasa, da ya kunshi yan wasa da suka fito daga Junior Katsina United FC.
Ya ce za a samar da wurin kwana da abinci ga dukkan yan wasan da aka gayyata.
Sanarwar ta bukaci yan wasan su nuna halin dattaku da da’a a lokacin aikin tantancewar, su kuma an basu tabbacin cewa, za a yi gaskiya wurin tantancewar.
“Hakan dai nada nufin bada dama ga yan wasan cikin gida da suka yi fice.”
Saboda haka hukumar gudanarwar kwallon kafar ta bayyana jin dadi ga kwamishinan wasannin jihar Katsina Dr. Bishir Saulawa bisa yadda yake ba yan wasan ƙwallon kafar jihar damar gwada hazakarsu.
Dr. Bishir Saulawa ya ce haka ne zai bunkasa kwazonsu da harkokin wasanni a jihar baki ɗaya.
