Kungiyar GMTD Zata Tallafawa Masu Kananan Sana’o’i 8,400 A Katsina
Kungiyar Grassroots Mobilization for Tunibu Dikko (GMTD) zata cigaba da baiwa masu ƙananan sana’o’i tallafi a fadin jihar Katsina
Ministan gidaje da raye birane Injiniya Muttaƙa Rabe Darma ne ya bayyana haka a lokacin bikin kaddamar da shugabannin kungiyar a Katsina
Ministan ya bayyana cewa an kafa kungiyar GMTD ne musamman domin karfafa goyon baya da gangamin siyasa ga shugaba Tinubu da gwamna Raɗɗa domin samun nasarar zaɓen 2027
Ministan ya ƙara da cewa daga watan yuni 2026 za su fara bada tallafi ga masu ƙananan sana’o’i kuma duk wata za su ba mutu 700, har tsawon shekara guda domin dogaro da kan su.
A cewar sa, bada tallafin na da nufin karfafa masu ƙananan sana’o’i domin su ƙara bunƙasa harkokin kasuwancin su musamman mata.
Injiniya Muttaƙa Darma ya bayyana cewa sun shirya tsaf domin fara gudanar da wannan aikin, wanda ya ce sun yi kyakkyawan tsari wajen tantance waɗanda za su amfana da tallafin.
“Za a yi rijista ne ta hanyar yanar gizo, domin kaucewa masu karɓar kuɗi a hannun jama’a da sunan za a ba shi tallafi, saboda haka duk wanda ya cike ƙa’idar mu zai amfana
Haka kuma ya ƙara da cewa inda mutum ya cancanta to babu abinda zai hana shi samu, sai idan mai nema ba, kuma ba wanda zai nema fiye da sau ɗaya.
A cewar sa, muƙamin ministan gidaje da raye birane da ya samu baya da gurin da ya wuce ya tallafawa al’ummar jihar Katsina da ƙasa baƙi ɗaya.
Ministan ya yi fatan al’umma za su cigaba da hakuri su kuma goyi bayan gwamnatin tarayya da kuma ta jihar Katsina musamman idan zaɓe ya zo na shekarar 2027
