Gwamna Raɗɗa ne yasa DSS suka tsareni Domin su murde mani takara – Hon. Ahmad Saleh
Ɗan takarar kujerar majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Bindawa da Mani ƙarƙashin jam’iyar APC Hon. Ahmad Saleh ya koka da cewa jami’an tsaron DSS sun tsare shi bisa umarni gwamna Raɗɗa.
Hon. Ahmad Saleh ya bayyana haka ne jam kaɗan bayan an bayyana Hon. Jamila Abdu Mani a matsayin wanda ta lashe zaɓen fidda gwani da aka gudanar a mazaɓu 22 na ƙananan hukumomin Bindawa da Mani da ke jihar Katsina
Dan takarar ya yi watsi da wannan sakamako inda ya ce babu wani zaɓen fidda gwani da aka shirya, tunda nasarar ce tun farko gwamna Raɗɗa ya kwashe.
Haka kuma Hon. Ahmad Saleh ya ce ba zai bar jam’iyyar APC ba, ya bar komi ga Allah sannan zai taimaka wajen samun nasarar shugaba Tinubu a zaɓen 2027
A nata bangaren gwamnatin jihar Katsina ta baƙin darakta janar na yaɗa labarai gwamna Maiwada Dammallam ya musunta wancan iƙirari na Ahmad Saleh wanda ya ce gwamna baya da ikon da zai sanya a tsare wani
Yana mai cewa hukumar DSS ce kawai zata iya ƙarin haske akan tsarewar da ya ce an yi masa, ya ƙara da cewa bashi da ma’ana ace gwamna yasa an kama dan takara.
Maiwada Dammallam ya cigaba bayanin cewa hukumar DSS ta gwamnatin tarayya ce, kuma suna ayyukan da suka shafi bincike da ka iya sawa aka mutum ko a tsare shi. Saboda haka ita ke da alhakin karin haske.
An dai bayyana Hon. Jamila Abdu Mani a matsayin wanda ta lashe zaɓen fidda gwani da kuri’a dubu 24,989 a ya yin da aka ce Hon. Ahmad Saleh Junior ya samu kuri’a 1,256
