An Tabbatar da Hamza Sule a Matsayin Ɗan Takarar Majalisar Wakilai na Kankara/Faskari/Sabuwa
Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a mazaɓar dan majalisar tarayya da ke Kankara, Faskari da kuma Sabuwa da ke Jihar Katsina sun tabbatar da Hon. Hamza Sule Faskari a matsayin ɗan takarar da zai fafata zaɓen majalisar tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027.
A wajen taron tabbatarwar da aka gudanar a Kankara, jiga-jigan jam’iyya daban-daban sun yaba da matakin kwamitin sulhu da ya amsa buƙatar shugabanni, mambobi da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC wajen zaɓen Hamza Sule a matsayin wanda zai ɗaga tutar jam’iyyar a mazabar.
Shugaban kwamitin sulhun, Tasiu Sabuwa, ya bayyana cewa matsayar da aka cimma ta samo asali ne daga ra’ayin masu ruwa da tsaki daga dukkanin gundumomi 31 na ƙananan hukumomin Kankara da Faskari da Sabuwa, waɗanda suka wakilci ra’ayoyin mambobin jam’iyya a yankunansu.
Alhaji Tasi’u ya ce daga cikin abubuwan da kwamitin ya yi la’akari da su akwai farin jinin ɗan takarar, yadda jama’a suka karɓe shi, jajircewarsa ga jam’iyya da kuma tarihin ayyukansa a siyasa da hidimar jama’a.
Ya ƙara da cewa Hamza Sule ya cika dukkan sharuddan da ake buƙata kuma idan aka zaɓe shi, zai wakilci al’ummar yadda ya kamata tare da ƙara wa jam’iyyar farin jini da goyon baya a tsakanin al’umma.
A nasa jawabin, mataimakin gwamnan jihar Katsina, Faruk Lawal Jobe, ya yaba wa kwamitin sulhun da kuma na shiyyar ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin gwamna, Tukur Ahmad Jikamshi, bisa gudanar da aiki cikin gaskiya da ƙwarewa.
Jobe ya roƙi waɗanda ba su samu nasara ba a zaɓen fidda gwani da su amince da matsayar kwamitin cikin mutunci tare da haɗa kai da sauran mambobin APC domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a babban zaɓe mai zuwa.
A jawabin karɓar takarar, Hon. Hamza Sule Faskari ya gode wa shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar bisa amincewar da suka yi wajen goyan baya ya wakilci ƙananan hukumomin Kankara da Faskari da kuma Sabuwa
Ya yi kira ga haɗin kai tsakanin shugabanni da mambobin jam’iyyar tare da buƙatar waɗanda ba su karɓi katin zaɓe na dindindin ba da su gaggauta yin hakan kafin babban zaɓen shekara mai zuwa.
Hamza Sule ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi domin wakiltar mazabar, zai bai wa harkar tsaro fifiko ta hanyar ƙara ƙaimi wajen samar da jami’an tsaro da kayan aiki tare da bullo da ingantattun hanyoyin yaƙi da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a ƙananan hukumomin uku na mazabar.
Hamza Sule ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan Muhalli har sau uku, sannan ya kasance Kwamishinan Albarkatun Ruwa sau ɗaya a jihar Katsina. Haka kuma ya yi aiki a matsayin Mataimaki na Musamman ga Sanatan da ke wakiltar shiyyar Funtua.
Baya ga harkokin siyasa, an san shi a matsayin fitaccen mai taimakon jama’a, ɗan kasuwa ne kuma gashi babban manomi. Yana riƙe da sarautun gargajiya na Wamban Faskari a Masarautar Faskari da Sadaukin Ƙasar Hausa a Masarautar Daura.
Masu sharhi kan harkokin siyasa a yankin na kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan APC saboda yawan magoya bayansa da kuma tallafin al’umma da yake bayarwa a faɗin mazabar.
