September 18, 2026

Yusuf Buhari Ya Halarci Zaɓen Fidda Gwani Na Sanatan Shiyyar Daura.

FB_IMG_1779108739702

Ɗan takarar majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Sandamu da Daura da kuma Mai’adua kuma tsohon ɗan shugaban ƙasa Hon. Yusuf Ibrahim ya halarci zaɓen fidda gwani a mazaɓar kangiwa da ke Daura.

 

Da ya ke jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala kirga al’ummar da suka hau layi domin cika sharuddan da jam’iyyar APC ta ayyana ma gudanar da zaɓen fidda gwani.

 

Hon. Yusuf Buhari ya bayyana gamsuwar sa bisa ga yadda al’umma suka fito domin gudanar da zaɓen fidda gwani na ‘yan majalisar dattawan na shiyyar Daura.

 

Kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Hon. Nasiru Yahaya Daura shi ne ke takara tare da Alhaji Ahmad Kabir (AK Canji)

 

Haka kuma ya bayyana fatan cewa al’umma za su goyi bayan jam’iyyar APC a duk zaɓuɓɓukan da ke tafe.

About The Author