September 18, 2026

Kungiyar ECOWAS Ta Ƙaƙaba Ma Jamhuriyar Nijar Sabbin Takunkumai.

0

Kungiyar ECOWAS ta ƙaƙaba wasu sabbin takunkumai saboda juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.

A baya dai kungiyar ta ECOWAS ta bai wa gwamnatin Nijar wa’adin kwanaki bakwai da ta maido da shugaba Mohamed Bazoum kan mukaminsa, ko kuma a sanya masa takunkumi, ciki har da daukar matakin soji, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust ta bayyana.

Sai dai masu juyin mulkin sun yi kira ga kungiyar ECOWAS da ya yi watsi da duk wani tsoma baki a kasarta.

Haka kuma sun yanke hulda da Najeriya, Togo, Faransa da Amurka, sannan sun rufe sararin samaniyar Nijar har sai abinda hali ya yi.

A karshen wa’adin, kungiyar ta shirya wani taro domin duba halin da ake ciki a yankin yammacin Afirka.

Da yake yiwa manema labarai jawabi a ranar Talata, mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngeale, ya ce an kara sanyawa wasu mutane da hukumomin da ke da alaka da gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar karin takunkumi.

Ko da yake bai yi cikakken bayani ba, ya ce an yi hakan ne ta hannun babban bankin Najeriya (CBN).

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *