November 18, 2026

Yadda Zaka Magance Matsalar Tsaron Zamfara: Shawarar Matawalle Ga Dauda Dare

0

Daga Hussaini Ibrahim

Karan Farko,tsahon gwamnan Jihar Zamfara,Bello Matawale ya ba Magajin sa gwamna Dauda Lawal shawara ,samar da Kwamishina na tsaro ko Mai bashi shawara akan tsaro da kuma tuntubar manyan Jihar da masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro da ke Jihar dan samun nasarar magance matsalar tsaron.

Matawale ya bayyyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi ga wakilan kafafen yada labarai da ke Zamfara a Lokacin da su ka kai masa ziyar tayashi murnar samun Minista a gidan sa da ke Abuja.

Acewar sa,Tsahon gwamna Matawale ya bayyyana cewa,tunda farkon rantsar da gwamna Dauda ya kamata ya sanya mai bashi shawara akan tsaro dan shine babbar matsalar da ta dabaibaye al’ummar jihar.dan jan kafa da gwamna Dauda ya keyi akan harkar tsaro tana kara jefa al’ummar jihar cikin mawuyacin hali.inji tsohon gwamna Matawale.

“Akan haka ne Matawale yayi kira ga gwamna Matawale da ya rinka tuntubar manyan Jihar irin su Sanata Abdulaziz Yari Abubakar da masu ruwa da tsaki a fagen Tsaro dan samun nasara dakile ayyukan “yan ta’adan.

Anasa jawabin Shugaban Wakilan Ungiyar kafafen yada labarai na Zamfara, Kwamaret Sani Haruna Dutsamma ya bayyyana cewa,ya fara da godiya ga Shugaban Kasa Ahmad Bola Tinibu da ya ba Hon Bello Matawale Minista da fatan Allah ya dafa masu wajan sauke ayyukan da aka bashi kuma ya shige masu gaba.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *