November 17, 2026

Kotu Ta Umarci INEC Ta Karbi Yan Takarar Jam’iyyar Labour a jihohi 24.

0

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a wannan Alhamis din ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta amince da sunayen ‘yan takarar jam’iyyar Labour Party LP a jihohi 24 na tarayyar kasar nan a babban zabe mai zuwa.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya bayar da umarnin ne a lokacin da yake yanke hukunci kan kararraki daban-daban da jam’iyyar ta gabatar a gaban kotu.

Kotun ta ce ya kamata INEC ta karba tare da fitar da jerin sunayen ‘yan takarar da jam’iyar LP ta miƙa mata daga jihohin da abin ya shafa.

Ta zargi hukumar zaben da saba wa sashe na 31, 33 da 36 na dokar zabe ta 2022, a lokacin da ta ki amincewa da jerin sunayen ‘yan takarar jam’iyyar LP bisa hujjar cewa shafin hukumar ya samu matsala.

Wasu daga cikin jihohin da hukuncin kotun ya shafa, sun hada da; Kwara, Plateau, Nasarawa, Lagos, Kaduna, Oyo, Benue, Bauchi, Ebonyi da Ekiti.

Sauran su ne; Katsina, Bayelsa, Niger, Rivers, Sokoto, Akwa Ibom, Gombe, Borno, Osun, Adamawa da Cross River, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard ta bayyana.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *