September 18, 2026

Kotu Ta Daure Matar Da Ta Zuba Ma Abiyar Zamanta Ruwan Zafi A Kwara.

0

Wata Kotun Majistare da ke Ilorin ta tasa keyar wata matar aure mai suna Lola Abdulsalam ‘yar shekara 42 da haihuwa a gidan gyaran hali bisa zarginta da zuba ruwan zafi a kan uwargidanta mai suna Bilikisu Abdulsalam.

Rahoton ‘yan sanda na farko ya bayyana cewa Lola wadda ita ce karamar matar, an ruwaito cewa ta wulakanci Bilikisu tare da cin zarafinta a lokacin da take kokarin cire mataccen bera a bayan ƙyauren gidansu.

Rohotonnin yan sandan sun kara da cewa wadda ake tuhumar ta fara dukan Bilikisu da tsintsiya, inda ta kira ta da mayya kafin ta shiga kicin ta samo tafasasshen ruwan zafi ta zuba km mata a jikinta, wanda ya sa fuskarta da gabanta suka kone sosai.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Zacheous Folorunsho, ya bukaci kotu ta ci gaba da tsare Lola a gidan yari har sai an kammala binciken ‘yan sanda akan lamarin.

A hukuncin da ya yanke, Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Dasuki, ya amince da bukatar mai gabatar da kara, kuma ya bayar da umarnin a tsare Lola a gidan gyaran hali na Oke-Kura da ke Ilorin, Jihar Kwara.

Majiyar Popular News Hausa ta jaridar LEADERSHIP ta bada rohoton cewa an garzaya da mamacin zuwa asibitin Olorunshogo, Ilorin, inda aka kwantar da ita domin jinyar konewar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *