Kotu Ta Kori Ƙarar Da Su Ibrahim Tafashiya Suka Kai Tsagin Sanata Yakubu Lado
Wata Babbar kotu ta 5 da ke Katsina ta kori karar da wasu magoya bayan jam’iyyar adawa ta PDP karkashin Alhaji Ibrahim Abdullahi Tafashiya inda suke nemna a soke zaɓen shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a shekarar da ta gabata.
Shari’ar da aka shafe kusan wata takwas ana kafsawa ta zo ƙarshe yau, inda mai Shari’a Alkali Abbas Bawale ya kori karar bisa dalilan cewa kotun sa bata da hurumin sauraran ƙarar.
Magoya bayan jam’iyyar adawa ta PDP da ke tafiyar gidan Dakta Mustapha Inuwa sun zargi tsohon ɗan takarar gwamna a jam’iyar PDP Sanata Yakubu Lado da yin uwa makarɓiya da jam’iyyar PDP abinda yasa suka garzaya gaban kotu domin neman hakkin su.
Da yake yanke hukunci, inda ya shafe kusan awa guda yana karanta irin shigar giza-gizai da tarin hujjojin da kowane bangaren ya gabatar a gaba kotun, a ƙarshe dai bayyana cewa kotun sa bata da hurumi akan wannan shari’ar.
Alkali Abbas Bawale ya bayyana cewa, kotun kolin Nijeriya da kuma kotun ɗaukaka kara duk sun yi hukunci cewa, kotu bata da hurumin sa baki cikin abinda ya shafi harkokin cikin gida na tafiyar da jam’iyun siaysa,
Ya ƙara da cewa, inda kotu ke iya shiga shine, idan aka zo zaɓen fitar da gwani akan batun takara, to idan an yi wa wani ba daidai ba, nan Kotuna ke iya shigowa domin samar da adalci.
A cewar Alkali Abbas Bawale, dukkannin bangarori sun gabatar da hujjojin su da kuma dalilai, amma dai matsayar babbar kotun jiha ta 5 shi bata da hurumi akan wannan ƙara saboda haka an koreta.
“Duk wanda bai gamsu da wannan hukuncin ba yana da damar daukaka ƙara nan da kwanaki 60 a gaban kotun ɗaukaka kara domin neman hakkin sa” inji shi
Tunda farko lauyan waɗanda suke yi ƙara wato bangaren Alhaji Ibrahim Tafashiya, Barista Mustapha Shitu Mahuta sun bayyana rashin amincewar su akan yadda aka hana magoya bayan su shiga zaɓen shugabannin jam’iyyar PDP a matakin runfa da karamar hukumar har zuwa jiha.
Barista Mustapha Shitu Mahuta ya ce wannan dalili yasa suka garzaya gaban kotu domin neman hakkin waɗanda yake wakilta a gaban shari’ar wanda ya ce indon ta a rufe yake.
Ƙarar mai lamba KTH/77/2024 an fara sauraranta a ranar 10 ga watan Agusta na shekarar 2024 inda tun a farkon zaman shari’ar lauyan waɗanda ake karar ya ce kotun bata da hurumin sauraran ƙarar, inda ya ce batu na cikin gida, saboda suna iya daidaitawa a tsakanin su.
Jim kaɗan bayan kammala yanke hukunci, lauyan waɗanda ake karar Barista Mustapha Shitu Mahuta ya ce ba su amince da wannan hukunci ba , saboda haka za su ɗaukaka kara domin neman hakkin su.
Yana mai cewa akwai wuraren da kotun ta amince da da’awar su, duk da cewa wasu wuraren kuma an samu aƙasin haka, amma dai a cewar sa suna da kwarin gwiwar samun nasara a kotun ɗaukaka ƙara.
