Kaura Namoda Zaya Fuskanci Matsalar Ruwan Sha Idan Ba a Ɗauki Mataki Ba
Daga Abdulrazaq Bello Kaura
KIRA NA MUSAMMAN GA MAHUKUNTAN KAURAN NAMODA DA JIHAR ZAMFARA DA MA DUK WANI MAI TAUSAYIN AL’UMMA.
Anyi wani nagartaccen tsarin bada Ruwan sha a Garin Kaura Namoda gari na Biyu mafi girma a jihar Zamfara, Wanda yanzu wasu da ga alama sun fifita biyan bukatar SU data al’umma, sun yi amfani da wata dama zasu tarwatsa tsarin Wanda a gaba al’unma zasu koka.
Akwai wani wuri da ake kira “RANJI” nan kusa ga ofishin LEA a garin Kaura Namoda, a wurin ne akeda wani babban Tanki “Overhead Tank” Wanda ake halbo ruwa daga Dam idan ya cika sai a Rarraba a anguwanni da yankunan Kaura Namoda, tau yanzu an samu wasu masu karfin hali sunyi kutse a wurin har sun rarrabe ma kan su filayen Wanda hakan babbar barazana ce ga sha’anin samarda ruwan sha.
A shekarun baya wani sanatan yankin ya nemo wani aiki akayi ginene da zimmar inganta samarda Ruwan shan, yanzu idan kuka mamaye wurin ya kuke son ayi?. Fisabilillahi
Wai sai sukayi dubarar bada cin hanci ga manyan mutane, kowa aka yanka mai nashi, don kar ace komi. Amma fa wannan bazai yi tasiri ba, don zamu wallafa sunan duk Wanda aka hada kai da shi don a zalunchi al’umma, don komi girman shi bai fi sauran mutane Daraja ba
ABUN LURA
Awannan wurin ne duka Manya manyan Bututun Ruwa wato “Pipes” suka ratsa suka wuce, akwai wasu cibiyoyi ne da ake rabon Ruwan wato “Valves” duka suna a wurin, AMMA A HAKA AKA RABE FILAYEN AYI GINI AKAN SU, KENAN IDAN GABA AKA SAMU WATA MATSALA BA BATUN GYARAN SU SAI DAI A SAKE WATA DUBARA saboda biyan bukatar wasu tsirarun mutane.
Duk da a zuwa yanzu ban samu sanayen wadanda aka rabawa filayen ba, amma da zarar na samu cikakken sunanyen SU zamu rubuta don a San su a kuma San kokarin cutar da al’umma da sukeyi.
Akwai takaichi, kwarorin mutane su rufe ido su cutar da Dubban mutane har kuma suyi tunanin samun gafarar ubangiji.
Annabi Muhammad S.A.W yayi gargadi na musamman akan cutar da al’umma a wurare uku HANYA da Inuwa da kuma MASHAYAR su (wato wurin da suke samun Ruwan sha)
Na biyu, Annabi Muhammad S.A.W yayi gargadi mai tsananin akan cin iyaka ko kwace filin wani, wanda yace “Duk Wanda ya zalunchi wani ko wasu da satar fili koda tsawon ‘Dani daya ne ko ace taki guda, tau a lahira za a daure shi da iggiyar wuta wadda tayi girman Duniya sau Bakwai.
Da haka muke kira ga shuwagabanni da suji tsoron Allah su kwato ma al’umma hakkin su, su hana wannan zalunchin da ake son yi, a kuma killache wurin don bashi kariya.
Mai son ya tabbata in har wadannan hotunan ba su wadatar ba, tau aje wurin a gani.
Duk wani mai kishin Kauran Namoda ko Kungiya ko hukuma ko gomnati ya dace yayi iyayin shi wajan hana wannan illar.
Abdulrazak Bello Kaura
Development Journalist
abdulkaura21@gmail.com
