September 17, 2026

Makarantar Islamayya Ta Hajiya Aisha Ta Mashi Ta Yaye Ɗalibai Guda 32

0

Daga Auwal Isah

Bikin yaye daliban dai ya gudana ne a farfajiyar makarantar dake cikin karamar hukumar Danmusa.

Da babban limamin Danmusa Malam Abu Sufiyan ke magana a wurin bikin yaye daliban, ya yaba ma sakataren gwamnatin jihar Katsina bisa gina makarantar don bunkasa ilimin addinin Muslumci.

Ya kuma yi bayani akan mahimmancin neman ilimin addinin Muslumci dana Boko.

Tunda farko, saida ya bada tarihin cewa Mustapha Muhammad Nwa ne ya gina makarantar a wasu yan shekaru da suka gabata.

Ya yi kira ga masu hali su kwai-kwaiyi irin wannan dabi’ar.

A nashi jawabin malam Darda’u Ma’azu Danmusa wanda yasa mu wakilcin magajin gari Sani Ma’azu Danmusa, ya yi godiya ga Allah SWA, tare da yaba ma sakataren gwamnatin Jihar katsina Mustapha Muhammad Nwa bisa sadaukar da gidan shi da aka gina islamiyyar.

Shi ma shugaban makarantar malam Aminu Umar Danmusa ya yi kira ga matasa su tashi tsaye su nemi ilimin addinin Muslumci

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *