Jihar Katsina Ta Cika Shekaru 38: Kungiyar CIoTA Ta Taya Gwamna Radda Murnar
Cibiyar Kula da Sufuri ta Nijeriya (CIoTA) reshen Jihar Katsina, ta bukaci al’ummar jihar da su hada kai da gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa wajen samar da ci gaba mai ɗorewa a jihar.
Buƙatar hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban CIoTA na jihar, Amb. Ibrahim Ahmed, a yayin bikin cika shekaru 38 da kafa jihar.
Sanarwar ta yi nuni da cewa gwamna Dikko Raɗɗa na samar da kyakkyawan jagoranci wajen samun ci gaba a muhimman bangarori, musamman ilimi, kiwon lafiya, bunkasa sana’o’i, da noma da samar da ababen more rayuwa da dai sauransu.
Sanarwar da Kuma jinjinawa Gwamnan kan irin yadda ya ba bangaren sufuri mahimmanci Kuma ya bunƙasa shi a cikin shekaru biyu kacal.
“A wannan muhimmiyar rana ta cikar jihar Katsina shekaru 28 da kirkirowa, muna taya dumbin al’ummar jihar murna kuma muna musu fatan alheri.
“Hukumar Kula da Sufuri ta Kasa, reshen jihar Katsina na mika fatan alherinta ga Gwamnan Jihar, Malam Dikko Umaru Radda PhD, kuma mun shaida irin ƙoƙarin da yake yi wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.”
Amb. Ibrahim Ahmed ya kuma bukaci al’ummar jihar su ci gaba da addu’o’i kuma kowa ya bada gudunmawarsa don ganin jihar ta ci gaba.
