Funtua Unity Foundation Ta yi alhinin Rasuwar Tsohon shugaban karamar hukumar Funtua
Daga Hussaini Yero, Funtua
Shugaban Kungiyar Hadikan Al’ummar Karamar Hukumar Funtuwa Watau (Funtua Unity Foundation) Kwamared Mannir Suleman Funtua ,bayyana kaduwar sa da alhininsa da rasuwar Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Funtuwa,kuma Tsohon Dan Majalisar Wakilai Hon Bishir Idris Nadabo (Fiya-Fiya) .
Kwamaret Mannir Suleman Funtuwa,ya kara da cewa,Rasuwar Hon Bishir Idris Nadabo gyibine mai wuyar cikewa .Kuma tarihi ba zaitaba mantawa da ayyukan cigaban al’umma da Hon Fiya-Fiya ya gabatar ba a tsohuwar Karamar Hukumar Funtuwa,Wanda ya hada da Kananan Hukumomi Funtuwa, Dandume Da Bakori.
Amadadin manbobin Kungiyar Funtua Unity Foundation muna mika ta’aziyyar ga Iyalan Marigayi Hon Bishir Idris Nadabo Fiya-Fiya da Mai daraja Gwamnan Jihar Katsina Dr Umar Dikko Rada Da Mai Martaba Sarkin Katsinan,Dr Abdulmumini Kabir da Sarkin Maskan Katsina Hakimin Funtuwa, Alhaji Sambo Idris Sambo da sauran ‘yan Uwa da abokan arziki.
Allah ya gafarta masa ya kuma albarkacin zuriyarsa amin.
