Cikar Jihar Katsina Shekaru 38: Gwajo-Gwajo Ya Lissafo Nasarorin Gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa
Mai baiwa Gwamna Dikko Umar Raɗɗa shawara na musamman kan harkokin siyasa, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo, ya taya al’ummar jihar murnar cika shekaru 38 da kirkiro jihar.
A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Katsina, Gwajo-Gwajo ya ce jihar na hannu na-gari a daidai wannan lokacin, karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda wanda ke ba da nagartaccen shugabanci.
“A wannan rana ta musamman ta cikar jihar Katsina shekaru 38 da kirkirowa, ina taya ɗaukacin al’ummar jihar murna, jihar ta samu nasarori masu yawa a wannan lokacin.
“Jagorancin Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D, ya kara harkaka jihar domin ya aza ta bisa harsashi na cigaba mai dorewa.
“Tun ran gini tun ran zane, daga lokacin da Malam Dikko Umaru Raɗɗa ke yakin neman zabe a mazaɓu 361 na jihar nan, ya gana da al’ummar waɗannan mazaɓun kuma nya ya rubuta bukatunsu, daga nan ya fito da taswirar ci gaba a kowane fanni, da Allah Ya ba shi Gwamna kuma ya fara aiwatar da wannan tsarin na cigaba.
“A kasa da shekaru biyu, Malam Dikko Radda ya gina tituna masu tsawon kimanin kilomita 70, ya kuma gina sabbin makarantu da dama, ya gyara wasu daruruwan makarantu, kuma ya debi malaman makaranta 7,200 aiki wanda ba a taba diban malaman makaranta masu wannan yawan ba a tarihin jihar nan.
“Ya kuma gina magudanan ruwa game da sauran ayyukan kawar da zaizayar kasa da kuma sanya fitilun kan titi a manyan biranen jihar.
“Ya kuma fadada hanyoyi da dama a cikin birnin Katsina a karkashin ayyukan sabunta birane wanda za a yi irinsu a Funtua da Daura.
“Ya gyara cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko guda 722 a mazabu 361 da ke fadin jihar tare da gina gidan likita a kananan asibitoci 361, ya kuma daga darajar wasu kananan asibitocin.
“Ya kuma horar da ma’aikatan noma 722, game da raba taraktoci, injinan feshi, injinan girbi da sauran kayayyakin amfanin gona da kuma tan 20,000 na takin zamani a daminar bana domin bunkasa noma.
“Ya kuma raba awaki 56,000 tare da abincinsu da sauran tallafi don bunkasa kiwon dabbobi a jihar.
“Malam Dikko Umaru Radda ya kuma karfafa tarbiyyar addinin Musulunci a jihar ta hanyar kafa hukumar Hizba, ya kuma daura harsashin bunkasa tattalin arzikin jihar ta hanyar kafa hukumar Zakka da Wakafi.
“Gwamnan ya samu nasarori da dama a cikin shekaru biyu kacal, ta yadda hatta da yawa daga cikin ‘yan adawa sun gamsu cewa akwai alkkbla a jagorancin jihar, shi yasa suka yi ta shigowa APC a ‘yan watannin baya”, in ji Gwajo-Gwajo.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da yi ma gwamnatin Malam Dikko Radda addu’a game da bada cikakken goyon baya.
