September 18, 2026

Cutar Ƙyanda: Za a yi wa Yara Miliyan 4.8 Allurar Riga-kafin Ƙyanda A Katsina

IMG_1865

Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Raɗɗa ta shirya tsaf domin fara allurar Riga-kafin ƙyanda da kuma ƙanwar ƙyanda (Rubella) a watan Oktoba, 2025.

Babban jami’in asusun kula da ƙananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, Rahama  M. Farah ya bayyana haka a lokacin wani taro da manema labarai akan gangamin da ake ƙoƙarin shiryawa dangane da wannan cuta a Katsina
Taron tattaunawa ya gudana tsakanin ‘yan jarida da jami’an kiwon lafiya wanda asusun kula da ƙananan yara na majalisar dinkin duniyar UNICEF da gwamnatin jihar Katsina suka ɗauki nauyin shirya ya maida hankali wajen irin gudunmawar da manema labarai za su bada wajen samun nasarar wannan gangami.
A cewar sa gwamnatin jihar Katsina ta samar da allura dubu 3,698,500 inda take hankoran yi wa yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar har miliyan 2.3 allurar Riga-kafin ƙanwar ƙyanda.
Rahama M. Farah, ya cigaba da cewa a wannan gangami da za a yi a watan Oktoba mai kamawa, ana sa ran cewa yara ‘yan wata tara zuwa shekaru 14 su kimanin miliyan 4.8 za a yi masu allurar Riga-kafin ƙanwar ƙyanda (Rebulla)
Haka kuma ya bayyana kafafen yaɗa labarai da cewa suna rawar da za su taka wajen wannan ƙoƙari na haɗin gwiwa domin samar da yanayin mai kyau ga yara
Kazalika Rahama M. Farah ya ce akwai tawaga kimanin 2,253 da za su jagorancin wannan allurar Riga-kafin ta hanyar amfani da wasu dibaru na wuccin gadi da za a fara daga ranar 4 ga watan Oktoba zuwa 13.
Da yake jawabi babban sakataren hukumar lafiya a matakin farko na jihar Katsina Dakta Shansudeen Yahaya ya bayyana cewa tattaunawar tsakanin ‘yan jarida da jami’an kiwon lafiya na da matuƙar mahimmanci ganin yadda cutar ƙyanda ke yi wa ƙananan yara fyaɗar ‘ya ‘yan kaɗanya
Ya ƙara da cewa sun gano jihar Katsina tana matsalar cutar ƙanwar ƙyanda (Rebulla) duk da cewa ana samun ƙarancin bayanai, sai ya ce amma yanzu an babbar dama zata tabbatar da kariyar yara.
“Zamu yi amfani da wannan damar da muke da ita yanzu wajen faɗakar da al’umma akan batun riga-kafi allurar foliyo wanda akasarin su yara ne daga haihuwa zuwa watanni 59” inji shi

About The Author