September 16, 2026

Jam’iyyar APC Ce Zata Cinye Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnonin a Nijeriya -Dikko Raɗɗa 

IMG-20260905-WA0054
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa jam’iyyar APC a dunkule take A jihar Katsina kuma ita zata yi nasara a zaɓen 2027
Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana haka a wajen ƙaddamar yakin neman zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmad Tunibu wanda Chief Oweizide Ekpemupolo (Tom Polo) yake jagoranta.
Take yaƙin neman zaɓen dai shi ne “PBAT door to door movement” inda aka ƙaddamar da kodinatoci 34 da shugaban ta na jihar Katsina Dakta Faisal Kaita.
A jawabin sa gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa jam’iyyar APC a jihar Katsina guda ɗaya ce, kuma ita ce zata samu nasarar a zaɓen 2027 mai zuwa.
Ya ƙara da cewa ya kamata al’ummar Katsina su cigaba da yi wa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tunibu godiya saboda irin sauye-sauyen da ya kawo a tsarin tafiyar da gwamnatin Nijeriya.

Gwamna Raɗɗa ya ƙara da cewa ya kamata su ci gaba da nuna godiya ga shugaba Bola Ahmed Tinubu, duk da masu hayaniya da ke ta surutu a kafafen sada zumunta suna sukar shugabanni su

“Insha’Allah, za mu kayar da su. za mu yi nasara cikin sauƙi, kuma In Sha Allah, za mu sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027.
Gwamnan ya yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce “ina so ka kwantar da hankalinka cewa jihar Katsina jiharka ce, kuma ba za mu ba ka kunya ba.
Malam Dikko Umar Raɗɗa wanda ya ce al’umma za su marawa shugaban Nijeriya baya a shekarar 2027 domin ya ci gaba da ayyukan alherin da ya fara wa ‘yan ƙasa.

About The Author