Jamhuriyar Nijar Ta Yanke Hulɗa Da Nijeriya Yayin Da Tattaunawa Ta Ci Tura.
Gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar ta yanke hulda da Najeriya bayanda kokarin kungiyar ECOWAS na sasanta ab da ke faruwa ya ci tura.
Kungiyar ECOWAS ta ba da wa’adin kwanaki bakwai na maido da shugaban kasar Mohamed Bazoum kan mukaminsa domin kaucewa rikici da gwamnatin mulkin soji.
Amma shugaba Bola Tinubu ya aika wata tawaga mai karfi zuwa kasar domin ganawa da shugabannin da suka yi juyin mulki, a ranar Alhamis.
Tawagar karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ta gana da wakilan gwamnatin mulkin sojan ne kawai.
Bayan haka dai, Nijar ta yanke hulda da Najeriya, Togo, Faransa mai mata mulkin mallaka, dama kasar Amurka
“An kawo karshen ayyukan manyan jakadun Jamhuriyar Nijar” a kasar Faransa, Najeriya, Togo da Amurka,” kamar yadda ɗaya daga cikin wadanda suka yi juyin mulkin ya bayyana a gidan radiyon kasa da kasa na Faransa.
A ranar 26 ga watan Yuli, hambararren shugaban jamhuriyar Nijar, Bazoum ya shiga hannun jami’an tsaron fadar shugaban kasa, kuma a yammacin ranar, sojoji suka sanar da cewa sun kwace mulkin kasar, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust ta bayyana.
