September 17, 2026

INEC Ta Nemi Goyan Bayan Sarakunan Gargajiya A Kano.

0

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta nemi goyan bayan masu riƙe da sarauyun gargajiya wurin wayar da kan al’umma don ganin sun amshi katin zabensu.

Kwamishinan hukumar zaben na jihar Kano Farfesa Risqua Shehu ya yi wannan rokon a lokacin da wani basaraken yarabawa ya kai mashi ziyarar ban girma, inji Popular News Hausa.

Farfesa Shehu wanda ya samu wakilcin sakataren mulkin hukumar Garba Lawal, ya ce akwai sama da katunan zabe dubu 400 da har yanzu ba a amsa ba a jihar Kanon.

Ya ce a karshen watan Oktoban wannan shekarar lokacin da za a gurza wasu sabbin katinan zaben, zai kasance Kano ita kadai nada katinan zabe miliyan 1 da ba a amsa ba.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *