Najeriya Ta Yi Barazanar Ficewa Daga ECOWAS.
Najeriya ta yi barazanar ficewa daga kungiyar kasashen yankin yammacin Afrika da aka fi sani da ECOWAS a takaice, idan kungiyar bata dakatar da daukar mutane aikin data ke yi ba a halin yanzu, inji Popular News Hausa.
Wakilan Najeriya a kungiyar suka yi wannan barazanar a Abuja a daidai lokacin da kungiyar ta yi burus da umarnin da aka bata, tare da maida hankali wurin daukar mutanen da suke so aikin, inda hakan ya saba doka.
Wakilan Najeriyar sun bada misali da irin dunbin kudaden da kasar ke kashe ma kungiyar ta ECOWAS duk da irin matsalar tsaron da Najeriyar ke ciki.
Sun ce Najeriya ba zata sake zuba kudinta a cikin kungiyar ba kamar yadda ta saba yi tun lokacin fara kungiyar a shekarar 1975.
Hakan dai na zuwa ne bayan da kungiyar ta ECOWAS ta gudanar da daukar aiki da ake zargin an yi san ran a cikin shi, da ya kai ga nuna ma Najeriya wariya.
Shugaban tawagar majalisar kuma mataimakin kakakin majalissar wakilan Najeriya Ahmed Idris Wase ya ce abu ne mai mahimmanci Najeriya ta yi bitar dangantakar ta da kuma matsayin ta a kungiyar.
