Idan Baka Da Jama’iyya Daga Shekarar 2015 Zuwa Yanzu….!
Daga Alƙalamin Yakubu Lawal
Na zaɓi in fara rubutu na da wannan taken, saboda ganin yarda muka ɗabi’antu da la’akari da siyasarmu da ƙabilarmu da addininmu ko dangantakarmu wajen nazarin ire-iren wannan rubutun a kafafen sadarwa.
Na tsaya nayi nazarin cewa idan zamu aje siyasa/jam’iyyar da muke ra’ayi (Partisanship) zamu ga cewa tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a wannan jamhuriyar, daga shekarar 1999 zuwa yau siyasar Najeriya ta buɗe sabon shafin da ‘yan ƙasa ya kamata su ɗauki darasin daidaita sahu don ɗorewa ita kanta ƙasar da al’ummarta.
Batu na farko da muka riska shi ne, ganin a shekarun da aka yi na dawowar mulkin dimokuraɗiyya,shi ne a karon farko samun nasara da rinjaye mai yawa da babbar jam’iyyar adawa ta yi da sunan zaɓin da al’umma suke so sannan aka miƙa mulki ga waɗanda suka ci zaɓe ba tare da tada jijiyoyin wuya ba.
Sai dai bayan nan, ƙalubale kala-kala suka kunno kai ga kusan dukkan ɓangarori na rayuwar masu mulkin da talakawa, a ya yin da masu mulki suke fama da rigingimun siyasa da ƙoƙarin kauda duk wani tarnaki da ka iya zama barazana ga kujerunsu da siyasarsu.
Wannan ya sanya wasu suka zaɓi ko dai canza gidajen siyasa ko jam’iyyar ma baki daya, to amman duk da ƙoƙarin kaucewa irin waɗannan matsaloli har yau har kwanan gobe waɗannan matsalolin sune suka yi kaka-gida suke ta bin masu mulkin da jam’iyyun na su.
Inda har wannan lokaci da muke na saura ‘yan kwanaki ayi babban zaɓe na shekarar 2023 babu jam’iyyar da ta samu nasarar dinke ɓarakokin da suke fuskanta ba.
A ɗayan ɓangaren,talakawa suma na kusan dukkan ɓangarorin ƙasar nan suna fuskantar ɗaya daga cikin ƙalubalen da ka iya kawo tarnaki ga jin daɗi da walwala na rayuwa kama daga rashin tsaro da rikicin addini da siyasa da rikicin ta’adanci da na ƙabilanci da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da makamantansu.
Duk da waɗannan matsaloli da har gobe ba su kauba ga masu mulkin balle ga talakawa mulkin dimokuraɗiyya daga shekarar 2015 ya kasance lokaci da gwamnatoci suka yi ayyuka na raya ƙasa da za a iya gani a nuna a dukkan matakai na gwamnati a daidaito iri ɗaya wato ( uniform infrastructure development)
Masu karatu za su yarda dani bisa ga cewa gwamnatin tarayya ta yi ayyuka da dama a ɓangarori daban-daban ko da cewa ayyukan ba su yi daidai da ra’ayinka ba, ko kuma ace ba a yi su inda ka ke so a yi ba.
Kazalika gwamnonin jihohi ma in muka yi masu kuɗin goro, ba tare da la’akari da jam’iyyar da suka fito ba, suma a jihohinsu sun yi rawar gani ta fuskar zuba ayyuka a ƙasa.
Masu karatu zasu ga wannan zance a fili da wannan misalan da zan yi da wasu jahohin Najeriya; misali a jihar Delta da Rivers da Bauchi da Borno sai Kano da Kaduna, ga mai bin kadin abubuwan da ka-je-ka-dawo kaɗan ne daga cikin misalan domin kusan mafi rinjayensu sun taɓukawar da ko da gwamnonin da suke mulkin ba ka ra’ayinsu a siyasance ka yaba da ɗaya daga cikin ayyukan da suka yi koda kuwa ba buƙatar al’ummar ba ce wannan aikin.
Waɗannan misalan sun nuna cewar, daga shekarar 2015, akwai cigaban ayyuka a bai ɗaya daga masu shugabanci da masu muƙamai a jam’iyyu daban-daban.
Sai ƙalubalen can dana faɗi a baya yafi tasiri a zukatan al’umma fiye da aikin da suke gani a ƙasa saboda dama duk al’ummar da ta rasa zaman lafiya da ilmi da lafiyar jiki da ta jikka, da kusan komai aka yi aƙasin su, duk darajar sa zai zamar masu ga koshi ga kwanan yunwa.
Wani abin da ke da ɗaure kai ga waɗannan matsaloli da suka ki ci suka ki cinyewa shi ne a kullum mahukunta batunsu shi ne suna bakin ƙoƙarinsu na ganin an ragewa al’umma/talakawa radaɗin matsalolin da ke sha masu kai.
Su kuma al’umma (talakawa) kullum kokensu shi ne ba su ji ba, balle su gani, wannan ne ya sanya abubuwa suka caɓewa masu mulki tare da ita ƙasar baki daya, .usamman yanzu da duk shugaba ke buƙatar yabo ba fallasa ba.
Shin ko Ina Matsalar take akan wannan al’amari? Ga fitilar ne ko ga Batir?
Alƙalamin Yakubu Lawal ɗan Jarida kuma
jami’in hulɗa da jama’a a Katsina.
