September 17, 2026

Hukumar Tace Finafinai Ta Buƙaci A Kawo Gyara Akan Ayyukan ‘Yan Fim

0

Hukumar tace Fina-finai ta jihar Kano ta buƙaci a kawo gyara dangane da yadda wasu hukumomin gwamnatin tarayya suke gudanar da ayyukan su kan ‘an masana’antar kannywood musamman jaruman Finafinan na Arewa, masu rubuce-rubucen littatafai tare da mawaƙan yabo da Nishaɗi.

Shugaban Hukumar Abba El-Mustapha ya bayyana hakan a lokacin ganawar sa da hukumomin kare Hakkin mallaka in da yake cewa, akwai hakkoki da dama da ya kamata a ce ‘yan masana’antar ta kannywood na amfana daga wannan hukumomin musamman masu sana’ar rubuce-rubucen littafai da mawaƙa da jarumai dangane da hakkokin su da ake karɓa daga wasu dai-daikun al’umma.

Ya ƙara da cewa baya ga kamfanoni da masu sana’ar downloading, don kuwa da yawa daga cikin ‘yan masana’antar ta kannywood ba sa amfana daga tagomashin wannan hukumomin inda ya buƙaci a kawo gyara a cikin tsarin.

A jawaban su daban-daban shuwagabannin hukumomin gwamnatin tarayya wato Alh. Sani Ahmad da Oga Moses Sun ce mawaƙa da dama suna amfana daga abin da hukumomin suke karba inda suka koka dangane da yadda mawaƙa da yawa daga cikin mawaƙan arewacin Nijeriya ba sa son yin rijista da hukumomin, sun kuma kara da cewa Haƙiƙa duk wanda ba shi da regista da Hukumomin doka ba ta bashi damar amfana daga abin da hukumomin suke samarwa ba .

Shima a nasa martani ɗaya daga cikin mahalatta taron wanda ya yi magana a madadin sauran mawaƙan Malam Adamu Hassan Nagudu ya nuna farin cikin sa tare da godewa hukumar tace Finafinan dangane da shirya taron irin sa na farko domin nema musu hakkokin su.

Taron ya Sami halartar mawaƙa da dama waɗanda suka haɗa da Nazifi Asananic da Adamu Hassan Nagudu da Husainin Danko da Ibrahim Rabi’u (Ikiram Kano) da dai sauransu

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *