Hukumar Kiyaye Hadurran Najeriya Za Ta Fara Kama Masu Banke Mata Jami’ai.
Hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya ta sha alwashin kamawa, tare da gurfanar da masu ababen-hawan da ke wulakantawa hadi da banke jami’an ta da ke bakin aikinsu.
Mataimakin babban kwamandan hukumar mai kula da babban birnin tarayya Abuja da jihar Niger ACM Shehu Muhammad ne ya nasar da hakan ga manema labarai a Abuja.
Ya bayyana cewa da damar masu ababen-hawan na wulakanta jami’an hukumar da basu da makami a lokacin da suke sauke nauyin da aka dora masu.
Ya ce hakan abun damuwa ne.
Kwamandan hukumar ya yi Allahwadai da wannan mummunan abun da ake yi ma jami’ansu akan hanya.
ACM Shehu Muhammad ya yi nuni da cewa, za su tabbatar da ganin ana hukunta masu aikata hakan yadda ya kamata.
Tare da shawartar masu ababen su riƙa bin ka’idoji da dokokin hanya don kauce ma hadari, sannan hukumar na mai bayyana cewa za ta ci gaba da aikin ta babu sani ba sabo.
