September 18, 2026

Hukumar Bada Ilimin Bai Daya Ta Bada Kwamfitoci Ga Makarantu.

0

Hukumar bada ilimin bai ɗaya ta jihar Katsina ta hori masu adana bayanai a makarantu su inganta aje bayanai yadda ya kamata, inji majiyar Popular News Hausa.

Shugaban hukumar Lawal Buhari Daura ne ya yi wannan horan a lokacin gabatar da kwampitocin tafi da gidanka wato Laptop ga jami’an da ke adana bayana a makarantu.

Ya faɗa ma sakatarorin ilimi cewa, an samar da kwampitocin ne domin ayi amfani da su a hukumance wurin tattara bayanai.

Da shugaban kungiyar sakatarorin ilimi Usman Umar Mai’adua ke magana a madadin yayan kungiyar, ya bayyana jin daɗi ga hukumar bisa raba kwampitocin.

Tunda farko, saida daraktan sashen tsare tsare, bincike da kuma kididdiga na hukumar Lawal Kofar Sauri wanda ya samu wakilcin jami’in hukumar mai kula da masu adana bayanan Shehu Abubakar ya ce an samar da kwampitocin ne karkashin shirin BESDA.

Inda ya ce hakan na da nufin inganta runbun tattara bayanai domin samun sahihan bayanan da jihar Katsina za ta yi aiki da su akan makarantu.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *