November 17, 2026

Hon. Usman Nadada: Maki Mai Sa Ayi Mamaki

0

Daga Garba Abu Abdullahi

wannan sharhi da kuma nazari game da rayuwar Hon. Usman Nadada na nuni da irin ƙyakkyawar alaƙarsa da jama’a musamman ‘yan jarida da sauran al’ummar, irin haka ya kamata ace kowane ɗan siyasa ko mai riƙa da muƙami a gwamnati ya kamata ace yana da su.

Ban taba mantawa, na san Kwamishinan Filaye da Safiyo na jihar Katsina, Alhaji Usman Nadada ta dalilin aikin Jarida.

Na fara haduwa da shi a ofishin sa lokacin ya na rike da matsayin Janar Manaja na Hukumar tsara birane da yankuna (tsohuwar KUPDA), a lokacin na nemi in mu’amalance shi yadda a ke mu’amalantar manyan mutane ma su rike da mukamai (Yallabai, Ranka Ya dade, Morning Sir da sauran su),

Kwatsam sai na ji shi ne ya fara bijiro man da maganar raha da zaulayata ta hanyar aiki na. Daga ranar na soma fahimtar ya na da matukar saukin kai da kokarin kulla mu’amala Mai kyau da Jama’a.

Na Yi aiki tare da shi kusan har na bar gidan talbijin na jihar Katsina, Wanda a wannan lokacin ban iya lissafa iya lokacin da ya dauki shawarar da na ba shi a kan yada labaru ko aiki da Yan Jarida a Hukumar shi.

Bayan na bar KTTV, kowa ya dauka cewa alaka ta kare kenan tsakani na da shi, tun da abinda ke Kai ni office din su yanzu babu shi, amma Alhaji Usman Nadada ya nuna ba Hakan ba ne.

Dan Wani lokacin ni ne ke ganin sakon shi na gaisuwar Juma’a ko sallah, ko kuwa Ina zaune kwatsam in ga ya kira ni a waya ya ce ya ji kwana biyu ba mu gaisa ba, har kunya ta kama ni kasancewar ni ya kamata in kira shi tun da ni ne karami.

Alaka ta da Maigirma Kwamishinan Filaye har ta Kai ya na daga cikin wadanda su ka rubuta man takardar halayya Ta-gari (certificate of good character), da hannun shi ba typing ba, wadda na kawo nan cikin takardu na a lokacin da zan kama aiki a Poly.

Ba ni sanya baki a hidimar ma su rike da mukaman siyasa, amma wajibi ne mutumin kirki a yabe shi, Dan Ina da yakinin cewa halin kirki da son kyautatawa mutane a cikin jinin Usman Nadada ya ke, ba wai siyasa ba ce.

Babban abinda zan iya tunawa shi ne Wani lokaci da ya giggina rijiyoyin burtsatse a yankin su da kewaye, domin saukakawa Jama’a wahalar ruwan sha da amfanin yau da kullum, baya ga daidaikun ayyuka da ya gudanar da Allah kadai ya San iyakar su.

Ko daga yanayin yadda mutane ke yabon shi, su ke kara ma sa adduar daukaka a rayuwa ka san maganar ta wuce siyasa.

A lokacin da na san shi ba Dan siyasa ba ne ma’aikacin gwamnati ne. A yanzu juyin al’amurra ya sanya ya zama Dan siyasa. Addua a nan ita ce:

  1. Duk abinda ya ke shi ne mafi alheri a wannan tafiyar Allah Ya tabbatar ma da Alhaji Usman Nadada shi
  2. Allah Ya karawa al’ummar mu mutane irin su Alhaji Usman Nadada, ma su son su ga Jama’a sun samu sauki da walwala a rayuwar su ta yau da kullum.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *