November 18, 2026

Hon. Sani Aliyu Ɗanlami Ya Gwamgwaje Matasa Biyu Da Aiki Gwamnati Na Dindindi. -Popular News

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Kwamishinan ma’aikatar Jindadi Da Wassani Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya yi abinda ya saba inda ya gwamgwaje matasa guda biyu da takardun kama aikin gwamnati na dindindi.

Wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da samun aiki ya zama wani baban ƙalubale ga ‘ya ‘yan talakawa.

Matasan guda biyu sun sami aiki ne a ma’aikatar Jindadi da Wassani ta jihar Katsina karkashin jagorancin Hon. Sani Aliyu Ɗanlami Mai raba Alheri.

Nura Abdu da Musty Opera suka samu wannan nasara kuma tuni sun karbi takardun kama aiki (Offers) kamar yadda doka ta tanada.

Da suke bayyana irin yadda wannan al’amari ya same su, sun fada da bakin su cewa babu abinda za su ce sai dai Allah ya saka masa da mafificin alheri.

“Abinda ka yi mana maina Allah ya yi maka. Inji Waɗanda suka samu Aiki a Ma’aikatar Jindadi Da Wassani” inji su

A madadin hukumar gudanarwa ta Popular News Hausa muna taya waɗanda Matasa murnar samun wannan aiki a ma’aikatar Jindadi da Wassani ta jihar Katsina karkashin jagorancin Hon. Sani Aliyu Ɗanlami.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *