Rashin Iya Aiki: Kwastam Sun Maƙalawa ‘Yan Sanda Sharri A Katsina
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina.
Rundunar’yan sanda ta ƙara reshen jihar Katsina ta musanta rahotanni da hukumar hana fasa kwabri ta ƙasa kwastam ta ce ta kama wani jami’in ɗan sanda yana fasa kwabrin shinkafa a Katsina.
Ta bakin kakakin rundunar SP Gambo Isah, ya ce ba su da bukatar jan wannan magana da take neman bata masu suna da hukumar kwastam akan wannan batu amma dai ‘yan sanda sun gano wasu abubuwa a lokacin binciken suka gudanar.
“Wannan mutum mai sune Surajo Zailani Abdulƙadir ɗan shekaru 41 da ke zaune a gida mai lamba 32 a layin Ahmad Dady Barakallahu G.R.A Kaduna wanda aka kama da buhun shinkafa 45 kuma aka ganshi da katin shaidar aikin ɗan sanda,karya yake ba jami’in mu ne ba” inji SP
Idan za a yi tunawa a jiya laraba ne hukumar hana fasa kwabri ta ƙasa reshen jihar Katsina ta gabatar da Surajo Zailani a gaban manema labarai inda ta ce jami’in ɗan sanda ne da yake aikin fasa kwabri a jihar Katsina.
Sai dai kuma bayan da hukumar kwastam ɗin ta mikawa rundunar’yan sanda shi kuma aka gudanar da bincike an gano cewa ɗan sandan bogi ne sannan yana ɗauke da katuna na shaidar aiki a wasu hukumomi na bogi cikin harda na ‘yan sanda.
Rundunar’yan sanda ta jihar Katsina ta cigaba da cewa ta yi mamaki da shugaban hukumar Kwastam ya ƙasa tuntuɓar kwamshiinan yan sanda akan batun kuma suka kasa gudanar da binciken kwakwaf kafin su yi tsallan bakaɗe su bayyana wanda ake zargi a matsayin ɗan sanda mai muƙamin ASP da ƙoƙarin ɓata sunan ‘yan sanda a idon al’umma.
Saboda haka rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina take kira ga al’umma da su yi watsi da wancan labarin na hukumar kwastam da aka buga a wasu jaridu cewa an kama ɗan sanda yana aikin fasa kwabrin shinkafa a Katsina.
Daga karshe SP Gambo Isah ya jaddada cewa za su maida wanda ake zargin ga hukumar hana fasa kwabri ta ƙasa da ke jihar Katsina domin ɗaukar mataki na gaba akan wanda ake zargi.
