September 17, 2026

Muna Buƙatar Al’umma Su Yi Aiki Da Jami’an Tsaro Dan Samar Da Zaman Lafiya -“Equal Access”

0

Daga Babangida Sunusi, Kano

Gdaunyar equal access hadin gwuiwa da kungiyar cleen shit suka gudanar da taron bada horo ga wasu daga cikin wakilan al’umma daga kananan hukumomin jihar Kano dasuka haxa da Ungoggo, Gezawa da karamar hukumar Nasarawa dan kara wayarma da sauran al’umma kai kan mahimmanci zaman lafiya ayankunan su.

Taron wanda yagudana a dakin taro na Tahir guests palace dake Nasarawa kano,yasamu halartar shuwagabannin addinai da masu rike da sarautun gargajiya da wakilan kungiyoyi dasauran jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki.

Dayake jawabi ga manema labarai mataimakin daraktan gidaunyar equal access na kasa mr Guard Peter Shamaki, yace bukatar wannan kungiya shine yadda zasu zama masu taimakama jami’an tsaro da duk wani goyon baya dazai iya kawo cigaba da zaman lafiya a yankunansu.

Shamaki yakuma cigaba da cewa lallai a jahar Kano sun fara dakko kananan hukumomin Nasarawa, Ungoggo da Gezawa dan kara jan kunnen al’umma dan kaucewa tashin hankali,inda yace kuma sunyi hakane dan bukata al’ummar da aka horar dasu rinka samun rana daya awata dan zama tare da shugabanin tsaro na yankin su domin tattauna matsaloli da kuma samo hanyar magance matsalolin.

Shima anashi jawabin wakilin shugaban karamar hukumar Gewaza Alhassan Danladi, yace qaramar hukumar Gezawa tana bakin kokarinta wajen taimakon ya’ya mata wajen karatunsu da tarbiyyarsu dan idan aka taimaki ya’ya mata to kamar antaimaki sauran al’umma ne baki daya.

Alhassan yakuma yaba da wannan kungiya ta equal access tayadda suke bakin gwargwado na taimakon jama’a wajen ganin sun samar da hanyar wanzar da zaman lafiya garesu dan haka itama karamar hukumar Gezawa ashirye take dan ganin tacigaba da hada kai da wannan kungiya tareda kungiyar cleen shit dan samarda cigaba mai dorewa ga al’umma.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *