Hakimin Mani Ya Hori Al’ummar Yankin Shi Da Su Ci Gaba da Kasancewa Masu Bin Doka Da Oda.
Durbin Katsina hakimin Mani ya hori al’ummar yankin shi da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda domin cigaban yankin dama jaha baki daya.
Umar Babani Isa ya yi kiran ne a lokacin da ya ke ma manema labarai jawabi a fadarshi.
Basaraken ya yi amannar cewa, karamar hukumar na daga cikin yankunan jahar Katsina dake da zaman lafiya, don haka ya bayyana bukatar ganin an hada hannu tsakanin da jami’an tsaro, yan sintiri da shuwagabannin al’umma don tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan yankin.
Hakimin ya yaba ma hangen nesan gwamnatin jihar Katsina da masarautar Katsina bisa dakatar da hawan sallah ta la’akari da matsalar tsaron da wasu sassan jahar ke fama fa su.
Ya kuma jaddada bukatar ganin al’ummar Musulmi na ci gaba addu’a a lokaci n sallah da kuma bayan an gama sallar don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a karamar hukumar da jiha dama kasa baki daya.
Umar Babani Isah ya yi amfani da bikin Sallar wajen tunatar da wadanda basu mallaki katin zabe ba, da su yi amfani da lokacin da ya rage su mallaki katin don zabar shuwagabanni nagari a babban zabe mai zuwa.
