An Hori Masu Dafa Abincin Yan Makaranta A Jihar Da Cewa Su Yi Aiki Da Masu Ruwa Da Tsaki Don Cimma Abinda Aka Sa Gaba.
Mai ba gwamnan jihar Katsina shawara akan tallafa wa rayuwar al’umma ya hori masu aikin dafa abincin yan makaranta da cewa su yi aiki da masu ruwa da tsaki don cimma abinda aka sanya gaba.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da magana da yawun sashen Abubakar Mamuda ya fitar.
Kamar yadda mai ba gwamnan shawara ya bayyana, jimullar dalibai sama da 800,000 ne ke amfana da shirin ciyarwar.
Abdulkadir Mamman Nasir ya kuma ce an dauki masu aikin dafa abincin sama da 10,000 a cikin shirin.
Ya bayyana bukatar ganin kwamitocin kula da shirin a matakin mazaɓun na sanya ido yadda ya kamata.
Sannan ya yaba ma shugaban kasa Muhammad Buhari da gwamna Aminu Bello Masari bisa kokari wurin bunkasa rayuwar marasa karfia cikin kasar nan.
