Gwamna Masari Ya Naɗa Muntari Lawal Muƙadashin Sakataran Gwamnatin jihar Katsina
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya amince da nadin Alhaji Muntari Lawal a matsayin muƙadashin sakataran gwamnatin jihar Katsina
Wannan yana kunshe ne acikin wata sanarwa da darakta janar na kafofin yaɗa labarai na zamani na gwamna Masari, Al’amin Isah ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai a Katsina
Haka kuma sanarwar ta ce Alhaji Muntari Lawal zai kama aikin sakataren gwamnatin jihar Katsina nan take.
Kafin bashi wannan muƙamin dai shi ne shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina.
